Yan Sanda biyu sun mutu a wani hari da tsagerun Biafra (IPOB) suka kai ofishin ƴan Sanda a Jihar Anambra.

Tsageru masu iƙirarin kafa ƙasar Biafra (IPOB) sun kai hari ofishin Jami’an ƴan Sanda a Jihar Anambra, yayinda harin yayi sanadiyar mutuwar aƙalla Jami’an ƴan Sanda guda biyu.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da yadda tsagerun na Biafra suka mamaye ofishin da misalin karfe 11 na daren jiya, yayin daga bisani suka samu nasarar bankawa ofishin wuta.

Jami’in hulɗa da Jama’a na rundunar ƴan Sanda a Jihar Anambra, DSP Tochuku Ikenga shine ya tabbatar da aukuwar lamarin ayau Alhamis, ya kuma ƙara da cewa Kwamishin ƴan Sandan Jihar ya samar da runduna ta musamman domin binciko masu hannu a faruwar al’amarin.

A ƙarshe; DSP Tochukwu Ikenga ya bayyana cewa gawarwakin Jami’an na ƴan Sanda guda biyu suna nan a adane, musamman a loƙacin da aka fara binciken ƙwaƙwaf dangane da faruwar al’amarin. “Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana”.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *