‘Yan sanda sun kama harsasai 753 masu matukar hatsari a Abakaliki, za a kai Abia

Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta kama wasu miyagun harsasan wata bindiga mai tarin hatsari a jihar.

Jami’an sun kama harsasan GPMG har 753 a wata motar haya da ta tashi daga Abakaliki za ta isa garin Umuahia na jihar Abia.

Frank Mba, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya yace suna tsananta bincike domin gano masu hannu a wannan safarar makaman Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi a ranar Lahadi ta kama wasu harsasai 753 na wata muguwar bindiga GPMG a jihar.

An boye harsasan a wani buhu wanda aka saka a wata motar haya daga garin Abakaliki, za a kaisu garin Umuahi na jihar Abia, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne yayin da hare-hare suka tsananta a kan jami’an tsaron dake yankin kudu maso gabas da kuma kudu kudu na kasar nan. ‘Yan bindigan da ake zargin mambobi ne na kungiyar IPOB ake zargi da wadannan hare-haren.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Frank Mba, a wata takardar da ya baiwa manema labarai a Abuja, yayi bayanin cewa an samu kama miyagun harsasan ne bayan bayanan sirri da suka samu.

Kamar yadda yace, tarewa tare da kama miyagun harsasan na daga cikin kokarin rundunar na dakile duk wasu ayyukan ‘yan ta’adda da kuma yadda ake samar musu da makamai a fadin kasar nan.

Mba ya jaddada cewa ana cigaba da ingantaccen bincike domin damke duk wadanda ke da hannu a cikin miyagun ayyukan.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *