Yan ta’adda sunyi gaba da mata ashirin a yayin da sukaje bikin suna a Jahar Katsina

Yan ta’adda sun sace mata ashirin a karamar hukumar dan dume ta jahar katsina a yayin da suka je suna a wani kauye mai suna Bido.

Wanna lamari ya faru ne a ranar juma’a.
Yan bindigan sun kuma kai hari a kauyen Unguwar Bawa ta karamar hukumar a inda suka saci wasu maza guda biyar.

Jahar Katsina na daya daga cikin jahohi na arewacin Nijeriya wadanda matsalolin ta’addanci suka fi shafa.

A ranar sha daya ga watan Dasumba a shekara ta dubu biyu da ashirin, yan ta’adda sun kwashi yara dalibai na makarantar kankara wadan da suka saki bayan sati guda.

Sannan kuma a sha tara ga watan dasumba, sunyi awon gaba da dalibai guda tamanin da hudu na Islamiyar Hizburrahim a karamar hukumar Mahuta amma basu jima ba aka sake su.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *