Labarai

‘YANCIN MATA: Bisa Adalci Yakamata ‘yan takara su dauki mata amatsayin mataimakan Shugaban kasa ~Cewar Aisha Buhari.

Spread the love

Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta bukaci jam’iyyun siyasa da su rika daukar mata a matsayin abokan takara ga ‘yan takarar da ke neman mukamai daban-daban a fadin kasar.

Aisha Buhari ta bayyana haka ne a daren ranar Asabar a lokacin da ta karbi bakuncin masu neman takarar shugaban kasa daga jam’iyyun siyasa daban-daban domin buda baki a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Uwargidan shugaban kasar ce ta shirya buda-baki da nufin samar da damammaki ga masu son raba soyayya da jin dadi da juna a cikin watan Azumin Ramadan da kuma kokarin gina kasa.

Ta ce yin adalci ga mata a harkokin siyasa shi ne tabbatar da cewa sun kara shiga cikin mukaman zabe.

A haƙiƙa, lokaci ya yi da za a ɗauki mata a matsayin abokan takara a kowane mataki idan aka yi la’akari da ƙarfin na jefa ƙuri’unsu da kuma tsunduma cikin harkokin siyasa.

“Yayin da muke tunkarar zaben 2023 da kyakkyawan fata, ina da yakinin cewa Najeriya za ta ci gaba da bunkasa daga karfi zuwa karfi a kan turbar dimokuradiyyarmu,” in ji ta.

Uwargidan shugaban kasar ta bukaci masu fatan zama shugaban kasar da su ci gaba da mai da hankali kan batutuwan da suka karfafa hadin kan al’ummar kasar, ‘yan uwantaka da hadin kan kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button