Yanzu Haka ‘yan ta’addan sun shirya suna son ayi sulhu da Gwamnatin Yana da kyau a basu hadin Kai ~Inji Sheikh Gumi.

Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya dage cewa tattaunawa da ‘yan fashi zai kawo karshen satar mutane da aikata laifuka a arewacin kasar da sauran sassan kasar.

Shahararren malamin addinin Islama din ya ce akwai bukatar gwamnati a dukkan matakai ta yi amfani da ‘yan ta’addan, ya kara da cewa (‘ yan bindigar) suna nuna alamun cewa a shirye suke su shiga tsarin Zaman lafiya.

Gumi wanda ya yi magana a wajen liyafar da ya shirya wa daliban 37 da aka sako na Kwalejin Gandun Daji da ke Kaduna, ya yi kira ga gwamnatoci da su yi hulda da ‘yan fashin don su bar ta’addanci.

Gumi ya ce, “Rokona ga gwamnati shi ne ta yi sulhu da’ yan fashin don ’yan fashin su bar hanyoyinsu na ta’addanci. Sun riga sun nuna alamun cewa sun shirya. Suna da korafe-korafe wanda nake ganin idan muka taru, zamu iya magance su, kuma mu magance wannan barazanar a cikin ɗan gajeren lokaci.

“Muna son hadin kan gwamnatocin tarayya da na kananan hukumomi, malamai da sauran‘ yan Nijeriya masu kyakkyawar manufa.

Ba ku yin shawarwari tare da abokinku; ka yi shawarwari da makiyinka. Abu na farko da zakayi shine ka gwada karya kankara ka karya shingen da ke tsakaninka da wanda kake tattaunawa da shi sannan kuma ka kara karfin gwiwa ta hanyar nuna cewa ba za ka yaudaresu ba.
Waɗannan mutane ne da suka daɗe suna cikin irin wannan laifin! dole ne mu yi amfani da ilimin halayyar dan Adam a kansu saboda ba zai yiwu dare daya a samu yardarsu ba.

“Amma yi musu wa’azi, tunatar da su da nuna musu hanyar fita daga matsalolinsu zai taimaka matuka wajen fahimtar da su da sakin yaran nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *