Labarai

Yanzu Likitana ya fadamin lokacin mutuwa ta shekaru biyar suka rage min a duniya ~Cewar Jaruma Kemi Afolabi.

Spread the love

Jarumar fina-finan Nollywood, Kemi Afolabi, ta ce likitanta ya shaida mata cewa za ta kara shekaru biyar ne kacal a duniya.

A wata hirar ta da wata ‘yar jarida Mai suna Chude Jideonwo, jarumar ta bayyana cewa ta kamu da cutar lupus.

Lupus wata cuta ce da ke faruwa lokacin da tsarin garkuwar jiki ya kai hari ga sashin gabobin jiki.

tabbas Ina da lupus. Kuma cuta ce ba shi da magani dole ne na cigaba da shan magunguna har tsawon rayuwar ta “

Jarumar ta kara da cewa ta kashe sama da Naira miliyan daya wajen yi mata magani amma ba ta samu sakamakon da ake bukata ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button