Yanzu muka Fara Aiki a jihar Gombe ~Inji Gwamna Inuwa Yahaya.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru biyun da suka gabata da cewa somin tabi ne, domin gwamnatin ta himmatu wajen samar da karin romon dimokiradiyya ga al’ummar jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Asabar din nan a filin wasa na Pantami yayin da yake jawabi, a bikin cikan sa shekaru biyu da zama zababben gwamnan jihar.

Ya ce gwamnatin ta samu nasarori da dama a bangarorin ilimi, da kiwon lafiya, da aikin gona, da inganta muhalli, da bunkasa karkara, da samar da ruwa, da gina hanyoyin mota, da tsaro da dai sauran su.

Gwamna Inuwa ya bawa al’ummar jihar tabbacin cewa gwamnatin sa ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin da take yi na ganin ta samar musu da ci gaba har inda suke a duk fadin jihar.

Manyan kusoshin jam’iyyar APC daga jihar dama Najeriya gaba daya, sun yaba da nasarorin da gwamnan ya samu, tare da tabbatar masa da karin goyon bayan su don ci gaba da nausa jihar gaba.

Sun kuma yi kira ga al’ummar jihar su marawa gwamnan baya a kokarinsa na kai jihar zuwa ga Tudun mun tsira.

Tun farko sai da gwamnan ya kaddamar da aikin sabuwar hanyar a Unguwar Kumbiya-Kumbiya, inda yayi kira ga al’ummar yankin su guji yin gini a kan hanya, yana mai gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta yi wata-wata ba wajen rusa duk wani gini da aka yi a kan hanyar, kasancewar ta riga ta biya diyya ga wadanda aikin hanyar ya shafa.

Haka kuma gwamnan ya aza tubalin gina makarantar Firamare da Karamar Sakandare ta Alabura a unguwar ta Kumbiya-Kumbiya, gunduma daya tilo a Najeriya da bata da makarantar firamare. Sai ya kira yi iyaye a yankin, su yi amfani da damar ta hanyar tura ‘ya’yansu zuwa makaranta, ganin cewa ilimi ya zo musu har gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *