Labarai

Yanzu mun Sami zaman lafiya a jihar Kaduna domin jami’an tsaro sun kori ‘yan ta’adda daga dajukan jiharmu ~Cewar El rufa’i.

Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce an samu sauyi mai kyau a harkar tsaro a jihar cikin makonni shida da suka gabata.

Ya ce tura dakaru na musamman da sojoji ke yi yana rage kai hare-hare a jihar.

A cewarsa, da a shekarun baya an yi amfani da hanyoyin da ake amfani da su a halin yanzu, da an samu zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da shirin gidan Talabijin na Channels Television da ke Kaduna a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da shirin Sunrise Daily.

Mikiya ta ruwaito cewa, ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga sun kashe daruruwan mutane yayin da wasu da dama suka rasa matsugunansu a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, a wani bangare na ta’addancin ‘yan boko Haram da suka addabi yankin Arewa maso Yamma.

‘Sojoji suna yin abin da muke fata’

El-Rufai dai ya dade yana tofa albarkacin bakinsa game da gazawar da hukumomin tsaro suka yi na magance ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.

Ya yi kira da a kai musu farmaki ta sama a yankunansu yana mai cewa ta haka ne kawai za a iya dakile wuce gona da irin su.

A cewarsa a jiya, duk abin da gwamnatin jihar ta bukaci jami’an tsaro da su yi a cikin shekaru biyu zuwa uku da suka wuce yanzu suna faruwa a jihar.

Gwamnan ya ce rundunar sojin kasar ta fitar da ‘yan bindigar daga jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button