Yanzu-Yanzu: Ahmed Musa ya bada gudunmawar miliyan 2 ga wata makaranta A Kano

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Ahmed Musa, Ya bayaar da gudunmawar kudi naira Miliyan Biyu (#2,000,000) domin gina masallaci a harabar makarantar sikandire ta Bokavo Barrack da ke Kano.

Ahmad Musa wanda tsohon dan wasan gaban CSKA Moscow ne ta kasar Rasha ya bada gudunmawar ne bayan ziyar tar makarantar da ya yi bayan kammala a tisaye da kungiyar da ake kira da Sai Masu Gida ta gudanar a yau Alhamis.

Haka zalika tsohon zakaran gasar kofin Afrika ta AFCON da ya lashe a shekara ta 2013,ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmawar gyara kujerin zama da suke makarantar.

Da ya ke ganawa da manema labarai Musa ya kuma yi kira da mahukunta a makarantar da su cigaba da gudanarda abunda ya kamata domin gyaruwar al’amuran makarantar da hakan zaisa al’umma da dama suyi kwadayin sanya ‘ya ‘yansu a makarantar domin samun ilimi addinin Musulunci a fadin yammacin arewacin Najeriya.

 Da ya ke jawabi ya yin karbar gudunmawar kudin, Daraktan makarantar Alhaji Yusuf Sa’idu nuna farin cikinsa ya yi da ziyarar da Ahmad Musa ya kai makarantar, da sakamakon zuwan nasa ya bada tallafin kudin da suke yi masa addu’ar fatan Alkhairi a rayuwarsa.

Haka zalika Alhaji Yusif ya kuma ce ziyarar Musa ta zo a daidai lokacin da suke bukatar gudunmawa, bayaga lissafa masa irin tarin matsalolin da suke cin karo da su ciki harda rashin ingancin ginin Masallacin da bandaki da rashin ajujuwa da kujerun zama a wasu daga cikin ajujuwan makarantar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *