Yanzu-Yanzu: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri

Mayakan kungiyar Boko Haram sun cinna wuta a wasu a gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Ana kuma jin karar harbin bindiga da abubuwa masu fashewa a sassan birnin daban-daban musamman kusa da Jiddari P.

Ana musayar wuta tsakanin sojoji da wasu da ake zargin yan ta’adda ne a kusa da Molai da Jiddari a babban birnin jihar.

“An ji a kalla karar abin fashewa uku a Maiduguri. Ana harbe-harben bindiga a halin yanzu, farar hula suna tserewa daga gidajensu suna tafiya hanyar Damboa da tsohuwar GRA,” a cewar majiyar tsaro.

Wani mazaunin garin da ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce bashi da wurin zuwa a halin yanzu saboda halin da ake ciki.

“A yanzu babu inda zan iya tafiya. Ba zan iya zuwa gida ba. Kana iya jin karar harbin bindigan?” in ji shi.

Ku saurari karin bayani …

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *