YANZU-YANZU : Masu garduwak da mutane sun saki ragowar Daliban Kwalejin Kaduna guda 27

Daliban makarantar nan 27 da ƴan fashi suka sace daga Kwalejin nan ta Tarayya, dake Afaka, jihar Kaduna, an sake su.

Ɗaya daga cikin mutanen da suka karɓi daliban ne ya tabbatar wa Aminiya labarin.
Ya ce kwamitin tattaunawa na Sheikh Abubakar Gumi ne ya taimaka wajen saki tare da goyon baya daga tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Ɗaliban na daga cikin mutane 37 da aka sace kusan watanni biyu da suka gabata.

Bayan biyan kuɗin fansa daga iyaye da shugabannin makarantar, ‘yan fashin sun saki 10 kawai daga cikin waɗanda aka yi garkuwar da su.

Tun da farko wadanda suka sace su sun nemi Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba su kudin fansa har Naira miliyan 500 amma Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da zabin tattaunawar, yana mai cewa ƴan ta’addan sun cancanci kashe su ne kawai.


Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *