Yanzu Yanzu: Pantami ya tsawaita wa’adin hade NIN-SIM har zuwa 30 ga watan Yuni

Sheikh Isa Pantami, ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani ya ce an kara wa’adin hade layukan SIM da lambar shedar dan kasa.

An tsawaita wa’adin shirin ne zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2021.

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa daga daraktan hulda da jama’a na hukumar sadarwa ta Najeriya da kuma Shugaban Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa.

Punch ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun hadin gwiwar daraktan hulda da jama’a na hukumar sadarwa ta Najeriya, Ikechukwu Adinde; da kuma Shugaban Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa, Kayode Adegoke.

An kuma tattaro cewa Pantami, wanda ya sha suka kan kalamansa na baya kan kungiyar Taliban, ya bayyana cewa an hada katunan SIM miliyan 54 da NIN.

A wani labarin, mun ji a baya cewa Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta ce ba za ta katse masu amfani da layin sadarwar ba sakamakon ci gaba da alakanta lambobin shedar kasa (NINs) da katinan SIM.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *