Yanzu Yanzu: Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta haramta tashe

A yau ne rundunar yan sandan Jihar Kano ta haramtawa masu yin al’adar nan tayin tashe a kowace Shekara a duk faɗin kafatanin lungu da saƙo na jihar Kano.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, shine mai magana da yawun ƴan sandan na jihar Kano, kuma shine ya sanar da wannan batu a yau ranar talata.

Rundunar ta bakin kiyawa, tace ta ɗauki wannan matakin hanawar ne sakamakon fakewa da ɓata gari sukeyi wajen fakewa da guzuma suna harɓin karsana.

A cewarsa, yawanci ɓata garin, nayin amfani da tashe ne domin aikata mummunar al’adar nan ta faɗan daba.Daga Ƙarshe, Haruna Kiyawa ya gargaɗi iyayen yara, dasu jawa ƴaƴansu kunne, domin kuwa rundunar ƴan sanda ta jihar Kano bazatayi ƙasa a gwuiwa ba wajen ƙwamushe duk wanda yayi kunnen uwar shegu da wannan sanarwa ba.

A cewarsa, duk wanda rundunar ta kama yana gudanar da al’adar tashe, babu shakka, rundunar zata ɗauki mataki akansa.

Abubakar Mustapha Kiru.

0 thoughts on “Yanzu Yanzu: Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta haramta tashe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *