Labarai
Yanzu-yanzu: Wani ginin bene ya ruguje a Legas, ana ci gaba da aikin ceto

Wani gini ya ruguje a kan titin Sonuga, Palm Avenue, a unguwar Mushin a jihar Legas.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Dakta Olufemi Oke-Osanyinyolu, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma’a.
Ya ce, “Wani gini ya ruguje a Mushin ‘yan mintoci da suka wuce. Ana ci gaba da aikin ceto.”
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a iya tabbatar da cewa wani ya makale a cikin baraguzan ginin da ya ruguje ba.