Yar aji shida a Firamare ta bindige Mai raino da dalibai 2

Wata daliba ‘yar aji shida ta bindige dalibai biyu da mi kula da su a wata makaranta dake jihar Idaho, a Amurka ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu, 2021.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa da kyar aka samu wani Malami ya kwace bindigan daga hannunta.

Shugaban yan sandan yankin, Steve Anderson, ya bayyana cewa dalibar ta harba bindiga a ciki da wajen makarantan.

Anderson ya ki bayyana sunanta kuma ba’a san dalilin da yasa tayi haka ba.

Yan aji shida a Amurka yawanci yan shekaru 11 zuwa 12 ne.

An garzaya da mutum uku da ta harba kuma ana kyautata zaton zasu rayu.

Dirakta a asibitin Eastern Idaho regional medical center, Dr Micheal Lemon, ya bayyana cewa an cire harsashin dake jikin mai kula da daliban kuma an fara jinya.

A cewarsa, harsashin ya sami mai kulan a kafa.

Amma daliban biyu na asibiti har yanzu kuma da yiwuwan a yiwa daya cikin aikin Tiyata, Dr Lemon ya kara.

“Yau mun ga abin tsoro da makaranta zai iya fuskanta,” wani jagora a yankin, Chad Martin ya bayyana.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *