Yar takarar jam’iyar APC Farfesa Nora ta lashe zaben sanatan Plateau ta kudu.

‘Yar takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben na sanatan Plateau ta Kudu, Farfesa Nora Daddut ta bayyana a matsayin wanda ta lashe zaben.

A sakamakon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar, Farfesa Nora ta samu kuri’u 83,15104 yayin da George Daika, abokin hamayyarta na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 70,838.

‘Yar takarar ta APC ta kayar da abokin karawar a kananan hukumomi hudu a yankin na sanata, yayin da dan takarar na PDP ya samu nasara a kananan hukumomi 2.

Leave a Reply

Your email address will not be published.