Zaɓen Shugaban Ƙasa 2023: A shirye muke damu tattauna da ƴan wasu yankunan don tsaida ɗan yankin mu takara- Ohanaeze

Shugaban gamayyar kungiyoyar inyamurai ta ƙasa wato Ohanaeze Ndigbo, George Obiozor, ya sanar da manema labarai cewar shekarar 2023, shekara ce ta inyamurai da zasu tsaida shugaban ƙasar Najeriya idan Allah ya kaimu.Obiozor yace, Inyamurai yan kabilar Igbo a shirye suke dasu tattauna gemu da gemu da sauran yankunan dake faɗin ilahirin wannan ƙasar a ƙoƙarin da suke na ganin Inyamurai sunyi shugabancin Najeriya a shekara ta 2023.

Obiozor ya bayyana haka ne a wani shiri da akeyi na wani gidan talabijin (TV) wato Arise Television.

Obiozor ya ƙara da cewa: Muna goyon bayan samun ɗan ƙabilar Igbo a matsayin shugaban ƙasa ɗari bisa ɗari. Kai shine ma mafi muhimmanci da zai faru da ƙabilar mu ta inyamurai. Mun hakikance daga karshe, lokacin mune yazo. Zamu jajirce tuƙuru domin ganin hakan ya samu damar faruwa.

“zamu tattauna da mutanen sauran yankin ƙasar nan domin su bamu daman. Saboda yin hakan ya dace, kuma abune dazai bada ma’ana bisa cancanta a lokacin daya kamata. Abune mai kyau, ace angama shirya komai izuwa yanzu, Shugabancin Igbo shine tsarinmu.”

Idan za’a iya tunawa, tuntuni Suleiman Ukandu, jigo a cikin jam’iyyar adawa ta PDP, yayi kira ga Kudu maso gabas dasu haɗa gwuiwa da sauran bangarori na Najeriya domin ganin 2023 an tsaida inyamuri shugabancin Najeriya.Ukandu shine tsohon Kwamishina na ƙasa da safayo daya ajiye aikinsa kwana kwanan nan, inda yace Inyamurai dole ne su fito su nemi tallafin sauran ɓangarori da yarurruka cewar zasu tabbatar da hadewar ƙasa a matsayin dunƙulalliya kuma al’umma ɗaya idan har aka basu dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *