Za A Fara Gwajin Miyagun Kwayoyi Ga ‘Yan Mata Kafin Daura Musu Aure.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa NDLEA ta bayyana cewa zata fara yiwa ‘Yan mata gwajin shan miyagun kwayoyi kafin a daura musu aure.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Shugaban hukumar Muhammad Mustapha Abdallah, ya bayyana haka a yayin da ake kona wasu miyagu kwayoyi da hukumar ta kama a Maiduguri.

Bikin kona kwayoyin an yi shi ne ranar Juma’a da ta gabata inda ya samu halartar gwamna Jihar, Babagana Umara Zulum.

Abdallah yace zasu hada hannu da Iyaye da malaman addini dan ganin an fara Gwajin kamar yanda ake gwajin kwayar kanjamau da kwayoyin Halitta itama miyagun kwayoyi a fara yin Gwajinsu kafin Aurar da ‘Yan Mata.

Shaye Shayen miyan Kwayoyi dai ya zama Tamkar Al’ada tsakanin Yara Mata a Kasar Nan.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.