Za a fara yiwa ƴan Najeriya alluran rigakafin cutar korona zagaye na biyu

KORONA: Za a fara yi wa mutane allurar rigakafin cutar a zango na biyu a Najeriya – In ji Shu’aib

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa Najeriya za ta fara yi wa mutane allurar rigakafin Korona karo na biyu a kasar nan.

Ya ce wadanda suka yi allurar rigakafin da farko ne za su dawo su kara yin allurar a karo na biyu.

Shu’aib ya fadi haka ne a taron da kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan Korona, PSC ta yi ranar Litini a Abuja.

Ya ce kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kara yawan kwanakin da mutum zai jira bayan ya yi allurar rigakafin cutar na farko daga makonni 12 zuwa tsakanin makonni 6 zuwa 12.

Shu’aib ya ce a yanzu haka manyan ma’aikata dake kula da yi wa mutane allurar rigakafin na tattauna hanyoyin inganta yi wa mutane allurar rigakafin a kasar nan.

“Hakan ya hada da tattauna matsalolin da suka yi fama da su yayin da ake yi wa mutane allurar rigakafin da farko sannan da tsaro hanyoyin kawar da su kafin a fara yi wa mutane allurar rigakafin karo na biyu.

Allurar rigakafin Korona

Shu’aib ya bayyana cewa zuwa yanzu mutum 1,690,719 ne suka mika kansu aka yi musu allurar rigakafin korona a kasar nan.

Hakan ya nuna cewa an yiwa kashi 84% na adadin yawan mutanen da ya kamata a yi wa rigakafin a kasar nan.

Najeriya na da burin yi wa akalla mutum miliyan 109 allurar rigakafin cikin shekara biyu.

Bayan haka Shu’aib ya ce za a yi wa mutane masu shekaru 18 zuwa sama allurar rigakafin korona a kasar nan.

An fara ne da jami’an lafiya, jami’an tsaro, ma’aikatan gidajen man fetur da sauransu allurar rigakafin.

Daga nan sai tsofaffi wadanda suka dara shekaru 60 zuwa zama.

Sannan sai sauran mutane.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *