Labarai

ZABEN 2023: Ku manta da batun addini ko kabila Yunwa ba ruwanta da batun addinin muslunci ko kiristanci ~Sakon Peter Obi ga ‘yan Arewacin Nageriya

Spread the love

A cigaba da Yakin Neman zaben sa a yankin Arewa Dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ya bukaci masu kada kuri’a a jihar Gombe da kada su yi zabe bisa addini ko kabilanci, yana mai cewa yunwa, fatara, rashin aikin yi da rashin tsaro ba su da alaka da kabilanci ko addini.

Obi, wanda ya ke gangamin yakin neman zabensa a ranar Laraba a Gombe, a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, ya shaida wa dandazon magoya bayansa cewa kwararre kuma shugaba mai tausayi ne kadai zai iya sake haifuwar Najeriya a wannan lokaci na tarihinta.

Idan suka ce ku zabe su don ’yan Arewa ne, ku ce musu yunwa muke ji, ku ce ba mu da aikin yi, ba mu da makarantu, ba ku da tsaro. Kuma dan arewa ne shugaban kasa?”. Ya tambaya.

“Shin akwai inda ’yan Arewa ke sayen biredi da rahusa? Haka abin yake ga mutanen kudu. Akwai inda musulmi suka sayi biredi mai rahusa? Akwai inda Kiristoci suka sayi burodi da rahusa? Kar ku zabe su saboda addini. Kada ku yi zabe saboda lokacin kowa ne. Lokaci ya yi da za ku kwato Najeriya.”

Dan takarar shugaban kasa na LP ya kasance a jihar tare da abokin takararsa, Datti Baba-Ahmed da sauran jiga-jigan jam’iyyar kamar babban masanin tattalin arziki, Pat Utomi.

Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya ce zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu zai Samar da sabuwar Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button