Labarai

Zaben2023: karku zabi masu Yanka masallatai ~Sanusi Lamido

Spread the love

Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi Lamido na II a wani bidiyo Dake yawo a kafafen sada zumintar zamani an hango Muhammadu Sanusi Lamido Yana bawa masu zabe shawara kan yadda zasu jajirce wajen zaben wa’yanda suke so ba wanda ya kwashe musu kudi ba.

Lamido Yana cewa yadda mutane su zabi wanda suke so ba wanda ya kwashe muku ku’din ba, mutun ya shekara hu’du Yana sayarda filayenku Yana sayarda masallatai Yana sayarda makabartunku Yana sayarda makarantunku Yana sayarda ganuwarku Yana asibitocinku ya tara ku’di yazo Kuma ya sayi zabe dashi.

maganganun na Muhammadu Sanusi Lamido sun jawo hankalin jama a wasu na Gani wannan Sako ne na Kai tsaye ga gwamnatin jihar Kano karkashin Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ake zargin gwamnatin da cefanar da wasu filaye mallakin gwamnatin.

A shekara ta 2020 ne Gwamna Ganduje ne ya tsige Sarki Muhammadu Sanusi Lamido bisa zargin rashin da’a ga gwamnati da Kuma rashin sanin Darajar masarauta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button