Zamu Dakatar da Dukkan Hare-haren Sojoji A Kasar Biyafara, Nnamdi Kanu Ya dau Alwashi

 Shugaban kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya ce karin tsoratar da gwamnatin Najeriya da sojojinta ke yi shi zaisa tabbatar da ballewar kasar Biafra a kusa.

Shugaban IPOB din a ranar Lahadi ya sha alwashin ba zai dakatar da tashin hankali ba kuma ya yi alkawarin daukar karin ma’aikata.

Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun fara farautar mambobin kungiyar tsaro ta Gabas, bangaren tsaro na kungiyar IPOB.

A yayin fatattakar ‘yan kungiyar IPOB da mambobin kungiyar ta ESN, an samu rahotannin kashe fararen hula a yankin Kudu maso Gabas, musamman a jihar Imo saboda ruwan bama-bamai ta sama da samamen kasa da jami’an soji ke kaiwa.

 Yawancin shugabannin Igbo sun soki gwamnatin Najeriya da sojoji kan wannan.

Sai dai, Kanu, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce kungiyar IPOB za ta dakatar da wannan kawanya idan gwamnati ba ta janye shi ba.

 “Bari wannan ya fito karara: Dole a daina wannan kawanyar da ake yi ma kasar Biafra.  Ko mun dakatar da shi.  Kewayen ba zai hana mu maido da Biafra ba. Sai dai ya kara ƙarfafa ƙudurinmu da ɗaukar ƙarin aminci ga lamarin. “Kanu ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *