Zamu Tsunduma Yajin Aiki Muyita Zanga-zanga Matukar Gwamnati Bata Rage Farashin Fetur Da Wutar Lantarki Ba, Inji Ƙungiyar Kwadago..

Kungiyar Kwadago ta Jadda Kudurinta ga Gwamnatin Tarayya kan, Fetur da Lantarki.

Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta ce ba gudu ba ja da baya ga shirinta na fara yajin aiki a ranar 28 ga Satumba saboda kin amincewa da gwamnati ta yi game da karin farashin man fetur da na wutar lantarki.

Majalisar Zartarwa ta kasa ta cimma matsaya a karshen wani taro da ta yi a Abuja yau Talata da rana.

A cewar shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Ayuba Wabba, ya yanke shawarar ci gaba da shirin da aka tsara na masana’antu wanda shugabannin kungiyar a fadin jihohi 36 da Abuja a kasar suka yi na tsunduma yajin aiki da zanga zanga don nuna kin amincewa sa kudurin gwamnati kan farashin Fetur da lantarki a kasar.

Idan kun tuna cewa, Hukumar Kula da Farashin Man Fetur ta sanar da karin farashin man fetur, yayin da Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya kuma ta kara kudin wutar daga N30.23 zuwa N62.33 a kan ko wanne KWH.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.