Labarai

Zan cigaba da taimakawa wajen Yaki da muggai masu kutse domin aikata miyagun laifuka a cikin Al’ummarmu ~Cewar Sarkin Zazzau.

Spread the love

Sarkin ya bayyana hakan a jiya ranar laraba a Lokacin da Sabon Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa reshen Jihar Kaduna, Malam Liman Sani Kila, ya kai wa Sarkin na Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ziyarar ban girma a fadarsa da ke birnin Zariya a Lokacin wannan ziyara ne Liman kila ya bayyana ire iren Ayyukan hukumar ga sarkin na zazzau.

Mai martaba sarkin Yasha alwashin bayarda da duk irin gudunmawar da hukumar ke bukata musamman a Kokarin ta na yaki da masu Aika muggan laifuka ta hanyar kutse ba bisa ka’ida ba.

Sani liman kila Wanda ya samu Karin Girma Babu jumawa zuwa matakin Kwanturola a hukamar ta kula da shige da fice an nada shi Kwanturolan jihar Kaduna ne Jim ka’dan Bayan samun Karin Girman.

kafin a Na’da shi Kila shine Mai kula da ofishin fasfo na Jihar Kano sani kila mutun ne wanda akayi shidarsa da aiki tukuru da Tsayuwa Kan magana daya tare da tsayar da Gaskiya da Riko Amana a aikinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button