Labarai

Zan kawo karshen kashe-kashen da satar mutanen dake faruwar a mulkin Buhari idan na zama shugaban Kasa ~Cewar Bola Tinubu

Spread the love

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya sha alwashin kawo karshen kashe-kashe da sace-sacen da ake yi a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na yanzu a Najeriya idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasar a watan Fabrairu.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana haka ne ayau ranar Litinin a lokacin yakin neman zabensa a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
“Za a kawo karshen kisa da garkuwa da mutane, kamar yadda” ya yi alkawari.

Tinubu ya kuma yi alkawarin samar da ayyukan yi ga matasa, samar da isassun kiwon lafiya, ingantaccen ilimi da sauran “fa’idodin ci gaba” idan aka zabe shi.

Tinubu ya halarci taron ne tare da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da suka hada da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ‘yar takarar gwamnan Adamawa a jam’iyyar, Aisha Ahmed wanda aka fi sani da Binani.

Za a gudanar da babban zabe a Najeriya a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 don zaben shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa da ‘yan majalisar dattawa da na wakilai.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kara da cewa jam’iyyar sa ba ta da maza bace kadai har da mata masu iya aiki kamar yadda ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su kada kuri’a ga Binani.

“Za mu yi muku aiki yadda ya kamata, za mu ba ku aiki yadda ya kamata,” in ji Tinubu ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar a wajen taron.

“Za mu kula da bukatunku, tare da Binani tare da Shugaban Kasa, Bola Tinubu insha Allahu (da yardar Allah), za mu kawo muku ci gaba, ilimi, lafiya, walwala, za ku samu ruwan sha mai kyau. Za a kawo karshen kisa da garkuwa da mutane.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button