Labarai

Zan kawo karshen PDP Kuma zan nuna masu Asalin waye ni idan sukayi kuskuren korana daga jam’iyar ~Cewar Wike.

Spread the love

Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce zai yi maganin jam’iyyarsa ta PDP, idan jita-jitar sallamarsa daga jam’iyyar ta zama gaskiya.

A cewar gwamnan, a lokacin ne shugabannin jam’iyyar adawa za su ga ainihin launinsa.

Wike, tare da gwamnoni hudu na jam’iyyar da aka fi sani da G5, sun dage kan cire Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Gwamnonin G5 sun hada da jihar Oyo Seyi Makinde, Samuel Ortom na jihar Benue, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, jihar Abia Okezie Ikpeazu da kuma shi kansa Wike.

Gwamnonin da ke korafin suna neman Ayu ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban jam’iyar ta PDP da sunan adalci kafin su marawa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP baya.

Wike wanda ya yi magana a cikin wata sanarwa a karshen mako, ya bayyana cewa zai mayar da martani da ya dace idan an kore shi daga jam’iyyar.

Bayanin nasa ya kara da cewa: “Sun ce za su kore ni. Ina ta neman ranar da za su kore ni Sai sun kore ni zan nuna masu barkono nake. Za ku sani cewa khaki ba leda bane”.

Wike Yasha alwashin kawo karshen jam’iyar PDP matukar sukayi kuskuren korensa daga jam’iyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button