Zan Tabbatar da an hukunta ‘yan fashin da suka Kai Hari A kauyakun Jihar Kaduna~ Inji Sanata Uba Sani


Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya ya ya ce Kashe-kashen Kidandan, Kade, da Sabon Sara na karamar hukumar Giwa  Dole ne a kawo wadanda suka aikata wadannan mugayen laifuffuka, Na yi matukar bakin ciki da samun labarin kisan mutane da yawa da lalata dukiyarsu a kauyukan Kidandan, Kade da Sabon Sara, duk a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna da wasu ‘yan fashi suka yi. Ina Allah wadai da kakkausan lafazi da wannan mummunan aikin na ɓatattun da Suka aikata.

Waɗannan laifukan cin zarafin bil’adama ne kuma bai kamata akyalasu ba tare an hukunta su ba Dole ne hukumomin tsaro su bi duk wani mataki don ganin an hukunta wadanda suka aikata wadannan munanan laifuka A daidai Wannan Lokaci Cikin gaggawa,  na gabatar da korafi a zauren majalisar dattijai ina kira ga jami’an tsaro da su kirkiro wasu dabaru masu inganci don magance karuwar barayin ‘yan ta’adda a karamar hukumar ta  Giwa  da sauran al’ummomin da ke fama da irin wadannan matsaltsalu. 
Abun takaici ne ace ‘yan fashi suna samun karfin gwiwa da rana tsaka, saboda haka muna  bukatar karin matakai masu tsauri. Sanatan ya Kara da Cewa Tunanina da addu’ata suna tare da mutanen Kidandan, Kade da Sabon Sara waɗanda wataƙila suna tunanin Babu matakin da za’a dauka na taimako a gare su a wannan lokacin. Kada ku yanke ƙauna. Muna tuntuɓar hukumomin tsaro don tabbatar da cewa ba a sake maimaita abin da akayi maku ba Ina kira gare ku da ku taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu na kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’a. 

Mai girma Gwamnanmu, Malam Nasir El-Rufa’i yana cikin matukar damuwa da kashe-kashe da barnata dukiya da ake yi kuma ya sha alwashin ba zai huta ba har sai an hukunta barayin. Ya kuma tattara hukumomin da ke da alhakin kula da gaggawa don ba da taimako ga mutanen da ke cikin damuwa na ƙauyukan Kidandan, Kade da Sabon Sara. Zan kasance tare da Gwamnanmu ko yaushe yayin da muke aiki don maido da wasu al’amuran yau da kullun ga kauyukan da abin ya shafa. 

Na yi wa Jami’an Mazaba cikakken bayani kan yadda za su gudanar da bincike game da bukatun mutanen Kidandan, Kade da Sabon Sara don taimaka min wajen yanke hukunci kan irin taimakon da zan bayar. Ina jin zafi kuma zan yi duk abin da zan iya don taimakawa a wannan lokacin na jarafta. 
Ina mika ta’aziyyata ga wadanda suka rasa ’yan uwansu. Allah Ta’ala Ya karfafe ku Sanata Uba Sani (Kaduna ta Tsakiya)

Leave a Reply

Your email address will not be published.