Zan Warware Duk Wani Takunkumi Da Trump Yasa Akan Musulmai, Inji Joe Biden

Zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya yi alkawarin dakatar da dokar Trump ta hana musulmai da bakaken fata shiga Amurka, Biden ya ce zai yi iyakar kokarinsa wurin ganin yayi adalci ga musulmai, wannan alkawarin nasa yasa musulmai da dama sun goya masa baya har ya samu nasara.

Dama tun hawan Trump mulki ya dakatar da kasashe kamar Iran, Libya, Somalia, Syria, Yemen, Najeriya, Sudan da sauran kasashe daga shiga Amurka.

Zababben shugaban kasar yayi niyyar soke dokar Donald Trump ta dakatar da matafiya daga kasashe 13, wadanda yawancinsu kasashen Afirika ne na musulmai.

A cewarsa, “A matsayina na shugaban kasa, zan yi aiki tare da ku don yaki da tsana wacce take tsakanin al’umma.

Mulkina zai yi iyakar kokarin ganin nayi adalci tsakanin musulmai da sauran ‘yan Amurka.

“A ranata ta farko a karagar mulki, zan dakatar da hana musulmai walwala.”

Dama Trump ya hana musulmai walwala.

Daga Ibrahim Dau Mutuwa Dole

Leave a Reply

Your email address will not be published.