Labarai

Zanga Zanga ‘yan fansho sun toshe kofar Gidan Gwamnatin Jihar Gombe.

Spread the love

Yan fanshon sun toshe babbar kofar gidan Gwamnatin Jihar Gombe, suna masu shan alwashin zaman dirshan har sai sun gabatar da takardar korafi ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.
Shugaban kungiyar ‘yan fansho na Najeriya (NUP), Muhammad Abubakar wanda ya jagoranci masu karbar fansho a zanga-zangar lumana, ya ce suna bin gwamnatin jihar bashin kyaututtuka na sama da shekaru tara bayan sun yi ritaya daga aiki.

Toshe kofar Gidan Gwamnatin Jihar ta dakatar da shiga da fita daga Gidan Gwamnatin.

‘Yan fanshon sun nemi a saka sauran membobinsu na kananan hukumomi 700 da suka yi ritaya wadanda suka bar aiki sama da shekaru biyu da suka gabata, amma ba a sanya su sahun Jerin masu karbar fansho na wata-wata ba.

Sun kuma zargi gwamnatin da rike fansho na karamar hukumar Gombe da suka yi ritaya sama da watanni hudu.

“Membobinmu sun ce yanzu Haka basu iya biyan kudin abinci, asibiti, kudin makaranta, kudin haya da kuma kudin magunguna.

Shugaban ya ce “Wannan ba zai yiwu ba kuma ba zasu Bari Hakan taci gaba ba saboda hakkokinmu ne muke nema.”

A lokacin rubuta wannan rahoton, gwamnan ko wasu jami’an gwamnati ba su halarci tsofaffin Yan fanshon ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button