Zantawa da mutumin daya shekara tara ya na zaman aure da aljana, yace zaman auren da daɗi, domin cikin minti goma kadai aljanar ta ke kai shi Makka.

Malam Ahmad Ali shine mutumin daya auri aljana, ya kuma haɗa su zaman kishi da ɗan adam mace.

YADDA SUKA HAƊU DA ALJANNAR

Kamar Malam Ahmad Ali Kofar Na’isa ya shaidawa majiyar Jaridar Mikiya, cewar abin ya samo asaline watarana a ƙofar Na’isa yayinda da mahaifiyar sa ta tafi ɗebo ruwa a rijiya, shi kuma yana yaro an goyashi.

Koda zuwanta domin ta ɗebi ruwa, sai ya kuɓuce ya auka rijiyar. Koda aka bincika domin asamo shi, sai aka nemi shi aka rasa.

Ashe aljana ce ta ɗauke shi, ta tafi dashi “Bahrul Aswad” na kogin “Nil” wanda yake a Misra.

Daga nan ne tayi ta rainonsa cikin aljanu, har Saida ya kai shekara 6, sannan ta ɗauko sa ta dawo dashi gaban mahaifansa dake nan ƙofar Na’isa.

Bayan yayi karance karance be, sai aljana ta yaba da hankalin sa, ta bashi auren ɗiyar ta mai suna “Ummu Subiyan” kuma yanzu haka cikin ikon Allah suna tare a matsayin mata da miji har na tsawon shekaru tara. Kuma cikin ikon Allah, auren Allah ya albarkace shi da samun ƴaƴa maza guda huɗu, duka an saka musu sunan daya dara da “Abdu, Abdu”, wato Abdulganiyu, Abdullatifu, Abdulwahabu da Abdurrahman.

TO KO TAYAYA YAKE RABA MUSU KWANA?Malam Ahmad Ali Kofar Na’isa ya ce, Litinin zuwa Juma’a shine lokutan matarsa Fatima, wacce itace mutum.

Sai kuma Juma’a zuwa lahadi shine lokacin aljana.

Kuma Malam Ahmad ya tabbatar da cewa, yasan kalan girkin da matarshi aljanna take so, kuma shi yake mata cefane idan lokacin ta yayi. Ballanta na ɗan adam.

KODA AKA TAMBAYI MATARSA FATIMA AHMAD CEWA TAYI

Ai suna hira da aljana, kuma ko kaɗan batayin kishi, hasali ma, bata tsoronta. A cewar ta:

Banajin tsoro a zaman mu da ita, sai dai ranar ta bana zuwa inda yake. Tana zuwan mun a siffar mutum ne, mu zauna muyi hirar mu da ita, harma mu ɓata lokaci, sai tace zata tafi”.

Malam Malam Ahmad Ali Kofar Na’isa ya kuma ƙara da cewa, ta sanadiyyar amaryasa aljana, yayi yawon buɗe ido, a sassan duniya da dama. A cewar sa:

“Ta sanadin ta, nasan ƙasar Saudiyya, nasan ƙasa a China, ana ce mata Beijing, sannan ta sanadin ta akwai wani waje a ruwa dana sani, ruwa baya shiga kuma baya fita a ciki ana ce masa “Bermuda triangle”.” Naje nayi hotuna, duk na ɗauko na taho dasu, sannan kuma munje katangar majuju wama juji.

“Kaga a saudiya, ni na maida ta kamar gida ne, muna zuwa masfala, Taf’an, arasaifa, afinkari, yamal da dai sauransu”.

“Kuma gabaki daya daga tashin mu daga nan Najeriya, zuwa Saudiyya yayi tsayin gaske minti goma. Tana cemin rufe idonka, buɗe idonka, zan ganni a duk inda muke son zuwa.” Inji Malam Ahmad

SHIN MALAM AHMAD ALI KOFAR NA’ISA YAYI KARATU?

Malam Ahmad yace yayi karatun “Aufaƙu” da “Magunguna” na gargajiya. Yayi kuma karatu a Maiduguri na shekara goma, Sannan yaje yayi karatu a Tahfeezul Qur’an dake Sokoto, tsahon shekara huɗu, inda ya karanci Fiƙhu. Sai kuma karatun da yayi a Misra a ƙarƙashin Abdul Fatihi Tuhi Falaƙ, inda ya karanci ɗibaka (harkan magunguna).

Sannan daga ƙarshe ya dawo jami’ar Bayero dake Kano inda ya karanci harshen Hausa, ya ƙware a ɓangaren “tsibbu” (Bori) da kuma “Ɗiffu” (Magunguna).

Domin kallon cikakkiyar hirar, kalli nan

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *