Zargin ta’addanci Majalisar wakilan Nageriya naso buhari ya tsige Pantami daga Minisata.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Ndudi Elumelu ya bi sahun masu kiraye-kirayen tsige ko murabus din Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dr Ali Isa Pantami.

Wannan ya Biyo Bayan  da tsoffin maganganun da ke cikin wa’azin Ministan wanda ke nuna tsattsauran ra’ayin addini.

A ranar Laraba ne dan majalisar ya tayar da batun a matsayin wani wuri na oda yana mai cewa ya keta alfarmar sa.

Ya lura cewa Ministan na da matukar tasiri kuma bai kamata a yi watsi da maganganun da yayi  ba.

Akwai kiraye-kiraye masu yawa na yin murabus ko korar Minista kan kalaman da ke nuna goyon bayan Taliban.

A martanin da ya mayar game da wannan, Ministan ya yi watsi da maganganun nasa na tsattsauran ra’ayi, yana mai cewa yanzu ya gane Gaskiya  amma duk da wannan, ‘yan Najeriya suna ta kara kiran a sallame shi ko kuma ya yi murabus.

Wannan ya haifar da ci gaba tare da Kira suna cewa, #PantamiResignNow

Jam’iyyar adawa, PDP ta kuma tayi kira ga Ma’aikatar Jami’an tsaron Farin Kaya ta (DSS) da ta gaggauta gayyatar Ministan don amsa tambayoyi sannan ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya kori Ministan nan take, “saboda la’akari da yadda batun ke cikin matsala.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *