Labarai

Labaran Safiyar Asabar 09/05/2020CE – 16/0/1441AH.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

An samu karuwar mutane 386 masu dauke da cutar Covid-19 a Najeriya, jimilla 3,912

Ma’aikatar lafiyan jihar Legas ta ce an sake sallamar mutum 42 da suka samu waraka daga cutar Coronavirus.

Jami’an tsaro na neman wani matashi dan shekara 25 da ya tsere daga cibiyar killace masu Coronavirus da ke jihar Bauchi.

Covid-19: Sarkin Musulmin Najeriya ya ce a saka takunkumi, a zauna a gida.

An Sallami Mutane 20 Da Suka Warke Daga Cutar Corona Virus A Jihar Gombe.

Gwaman Badaru na jihar Jigawa ya bayar da umurnin bai wa duk almajirin da yake killace Naira dubu goma-goma.

Gwamna Yahya Bello na jihar Kogi ya ce jami’an NCDC sai sun killace kansu na kwanaki 14 kafin su yi aiki a jihar.

Jumillar mutum 35,432 ne suka kamu da cutar Covid-19 a Saudiyya.

Mayakan Haftar sun fara mika wuya ga sojojin gwamnatin Libiya.

Wani jirgin sama kirar Rasha mallakar Rundunar sojojin saman Indiya ya fado a jihar Pencap da ke kasar.

Fararen hula 4 sun rasa rayukansu sakamakon ruwan bama-bamai a jihar Hajja da ke Yaman

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button