Labaran Safiyar Jumma’a 08/05/2020CE – 15/9/1441AH.

Daga Haidar H Hasheem Kano
An samu karuwar mutane 381 masu dauke da cutar Covid-19 a Najeriya, jimilla 3,526.
Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu ‘yan Najeriya na wasa da cutar Coronavirus.
Hukumar INEC ta agaza wa Jihar Sokoto a yaki da cutar Covid-19 a jihar.
Shugaba Buhari ya amince a sayo kayan aikin lafiya daga kasashen waje.
Gwamna El-Rufa’i na jihar Kaduna ya ce Gwamnonin Arewa sun shirya hana almajiranci a jihohinsu.
‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a kauyukan Faskari da Batsari a jihar Katsina.
Coronavirus: Ministan lafiya ya ce Najeriya za ta yi amfani da magungunan gargajiya don magance cutar.
Mutane 55 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan sama a Ruwanda.
Iskar gas mai guba ta yi ajalin mutane da dama a Indiya.
Hamshakin dan kasuwa a Rasha, Dmitriy Bosov ya kashe kansa.
Bayern Munich ta nada Miroslav Klose a matsayin mataimakin koci kan kwantiragin kaka daya.