Lafiya

Labaran Safiyar Litinin 11/05/2020CE – 18/0/1441AH.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

An samu karin mutum 248 sun kamu da Coronavirus a Najeriya, jimilla 4,399.

Gwamnatin jihar Borno ta ce an sallami mutum 12 daga asibiti bayan sun warke daga cutar Coronavirus.

An gano mutanen nan guda 2 da suka tsere daga inda aka killace bayan an same su da cutar Covid-19 a Kaduna.

Covid-19: Ma’aikatan lafiya ta yi shelar cewa duk mai maganin gargajiyar da ya gano maganin cutar, ya kai wa NAFDAC samfuri.

Almajirai 200 za a mayar garuruwansu bayan sun yi kwanaki 14 a killace a jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da rasuwar kwamishinan filaye da gidaje Surajo Gatawa.

Mutane 3 sun rasa rayukansu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai jihar Katsina.

Gwamnatin tarayya ta kwaso ‘yan Najeriya 150 da suka makale a Amurka sakamakon Coronavirus.

Hukumar dakile cututtuka ta Tarayyar Afirka CDC ta ce mutum 61,181 suka kamu da cutar Covid-19.

Gwamnan Tillaberi a Jamhuriyar Nijar ya ce ‘yan bindiga a kan babura sun kai hara-hare inda suka halaka mutum 20.

Covid-19: Cutar ta kara bulla a Wuhan na China inda ta samo asali.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button