Labarai

Labaran Safiyar Litinin 18/05/2020CE – 25/0/1441AH.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Shugaba Buhari zai yi wa al’ummar kasa bayani a yau kan cutar Covid-19.

An samu karin mutane 338 masu dauke da cutar Covid-19 a Najeriya, jimilla 5,959.

Jigo a jam’iyyar APC, Danbalki Kwamanda ya ce Shugaba Buhari ya rasa farin jininsa.

Gwamnatin tarayya ta damka tallafin fiye da tirela 120 na kayan abinci ga gwamnatin jihar Kano domin a rabawa jama’a.

‘Yan bindiga sun kai hari a garin Bilbis da ke karamar hukumar Tsafe jihar Zamfara ana gab da shan ruwa a jiya.

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta rika biyan masu rike da mukaman siyasa a jihar rabin albashi sakamakon kalubalen cutar Covid-19.

Jami’an tsaro a jihar Cross River sun tarwatsa wani taron daurin aure da ake cikin gudanarwa a wani coci a jihar.

Shugaba Buhari ya bai wa sojoji umurni su yi wani shiri na musamman domin kawar da ‘yanbindiga a jihar Katsina.

Gwamnatin jihar Oyo ta rufe wani kamfani bayan da ma’aikatan kamfanin 30 suka kamu da Coronavirus.

Covid-19: Mutane 88,709 suka mutu sakamakon cutar a Amurka.

Coronavirus: Firaministan Ingila Boris Johnson ya ce ya kamata a bar musulmai su yi shagulgulan Sallah,.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button