Labaran Safiyar Talata 12/05/2020CE – 19/0/1441AH.
Daga Haidar H Hasheem Kano
An samu karuwar masu dauke da cutar Covid-19 a Najeriya 245, jimilla 4,641.
Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 17 a Kaduna.
Sakataren Gwamnatin tarayya, ya ce Buhari ya bayar da umurnin a karbo maganin Coronavirus daga Madagascar.
Gwamna Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da raba wa mutane takunkumin fuska milyan daya.
Akwai yiwuwar Gwamnatin tarayya ta rage yawan ma’aikata a Najeriya.
Covid-19: Mutum na farko ya mutu da cutar a jihar Gombe.
Coronavirus: Matasa sun yi wa jami’an kotun-tafi-da gida dukan tsiya a Taraba.
Mutane 9 suka mutu a wata gobara da ta tashi a gidan kulawa da tsofaffi na Rasha.
Covid-19: Kasar Saudiyya ta sauke tallafin wata-wata ga ‘yan kasa, ta kuma ninka kudin haraji.
‘Yan bindiga sun budewa masallata wuta a Afghanistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3.
Ahmad T Adam Bagas makeup mens M Inuwa MH Sabiu Danmudi Alkanawi suits