Labaran Yammacin Alhamis 14/05/2020CE – 21/0/1441AH.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Shugaba Buhari ya yi taron gaggawa da shugabannin hafsoshin tsaro.
Covid-19: Gwamnatin jihar Gombe ta janye dokar hana sallar jam’i.
Gwamnatin tarayya ta rage kasafin kudin 2020 zuwa Naira Trilyan 10.523
Rundunar sojojin Najeriya sun ce sun kashe ‘yan Boko Haram 9 a jihar Borno.
Masu dauke da cutar Coronavirus sun yi zanga-zangar rashin abinci a jihar Nasarawa.
Gwamnatin jihar Rivers za ta gina makarantu a harabar da ta rushe otel-otel.
Gwamnatin tarayya na nazarin karbo bashin euro bilyan 1 don inganta noman zamani.
An sallami Sarkin Daura, Umar Farouk daga asibiti bayan ya warke sarai.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kara sukar yadda China ta tafiyar da cutar Coronavirus, yana barazanar kawo karshen alakarsa da China.
Japan ta janye dokar kulle da ta sanya sakamakon cutar Coronavirus a mafi yawan yankunan kasar.
Burundi ta kori wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya a kasar da kuma ma’aikatan lafiya uku daga kasar.