Labaran Yammacin Lahadi 10/05/2020CE – 17/0/1441AH.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Hukuma NCDC ta ce an samu karin cibiyoyin gwajin cutar Covid-19 guda uku a Najeriya.
Gwamnatin jihar Legas ta ce karin mutum 21 sun warke daga cutar Coronavirus.
Dokar Kulle: Kamfanonin sufuri masu zaman kansu sun ce sun yi asarar Naira Trilyan 3 a tsawon makonni 5 na dokar a Najeriya.
Al’ummar Fulani a jihar Delta sun bukaci a biya su diyyar kona masu gidaje da aka yi.
Gwamna Wike na jihar Rivers ya jagoranci rushe wasu Otal 2 da suka karya dokar kulle a Fatakwal.
An samu karin mutum karin 7 da suka warke daga cutar Coronavirus a Abuja.
Wasu mutane 2 masu dauke da cutar Coronavirus sun tsere a Kaduna.
Sheikh Bala ya karyata rahotannin mutuwarsa da ake yadawa, ya ce yana nan lafiyarsa lau.
Covid-19: Wadanda suka kamu da cutar sun zarta 200,000 a Rasha.
Ministan lafiyar Jamhuriyar Kamaru, Malachie Manaouda ya ce kasar na da mutum 2579 masu dauke da cutar Covid-19.
An kaiwa Masallaci hari da duwatsu a garin Cologne da ke Jamus.