Labaran Yammacin Lahadi 17/05/2020CE – 24/0/1441AH.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Gwamna El-Rufa’i na jihar Kaduna ya nemi gafarar wadanda suka kuntata da dokar hana zirga-zirga a jihar.
Covid-19: Ministan jiragen sama, Hadi Siriki ya ce an kama jirgin Ingila da ya saba doka a sararin samaniyar Najeriya.
Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da motocin yaki 10, sun kashe dakaru 5 a jihar Borno.
Covid-19: Mutane 3 daga cikin ‘yan Najeriya da aka kwaso daga Dubai na dauke da cutar.
Mutum 23 sun warke daga cutar Coronavirus a Abuja cikin awa 24.
Covid-19: Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta mayar wa da kamfanin ExxonMobil tallafin motoci 10 da ya bayar.
Gwamnatin Jihar Filato ta koka kan yadda wasu mazauna jihar ke bugo katin izinin yin zirga-zirga a jihar na jabu.
Coronavirus: Gwamnatin jihar Lagos ta killace mutane 39 da suka dawo daga Ghana
Covid-19: Kasar Indiya ta kara wa’adin dokar kulle da ta saka a kasar da mako biyu.
An taras da gawar Jakadan China a Isra’ila, Du Wei a gidansa.
Kungiyar Man United za ta iya yin asarar fan miliyan 140 idan aka ci gaba da wasa babu ‘yan kallo.