Labaran Yammacin Litini 11/05/2020CE – 18/0/1441AH.

Daga Haidar H Hasheem Kano
An samu karin mutane 33 da suka warke daga cutar Coronavirus a jihar Lagos.
Gwamnatin tarayya ta ce cutar Covid-19 ne ta kawo jinkirin biyan sojoji da sauran jami’an tsaro albashin watan Afirilu.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe ‘yan fashi 17 a gari uku a karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Ma’aikatan tasoshin ruwa, Maritime sun barazanar shiga yajin aiki idan Gwamnatin jihar Rivers ba ta sako membobinta da ta kamata ba.
Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya ce tsananin zafi ne ya haddasa mace-mace a jihar.
Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana aniyarsa ta janyewa daga harkokin siyasa domin mayar da hankali kan ayyukan jinkai.
Hukumar leken asiri ta Afghanistan ta ce ta kama shugaban kungiyar ISIS na yankin kudancin Asiya
Shugaba Putin na Rasha ya sanar da dage dokar kulle daga ranar Talata, duk da yaduwa da cutar Covid-19 ke ci gaba da yi.
Kasar Kenya ta saki fursunoni 7,000 a wani mataki na rage cunkoso a gidajen yarin kasar sakamakon Covid-19.
Coronavirus: Mataimakin Shugaban Kasar Amurka, Mike Pence ya kebe kansa.
Girgizar kasa mai karfin awo 5.5 ta afku a jihar Ibaraki da ke gabashin Japan.