Labarai

Labari da Dumi dumi Osinbanjo Yace dole su bude Bodojin Nageriya

Spread the love

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Gwamnatin Tarayya na iya sake bude iyakokin kasa nan ba da jimawa ba. Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a watan Oktoba na shekarar 2019 ya ba da umarnin rufe kan iyakoki don duba matsalar safarar kayayyaki da makamai da alburusai cikin kasar da kuma kare harkokin kasuwancin cikin gida. Lamarin da yaja CeCe kucen ‘yan Kasa daban-daban daga ƙungiyoyin ƙwararru, masana tattalin arziki da ɗaiɗaikun mutane. Shugabannin kasashe kamar Ghana da Jamhuriyar Benin sun kuma yi kira ga Shugaban da ya sake duba batun rufewar,
Amma Shugaban ya ci gaba da cewa iyakokin za su kasance a rufe har sai an duba rahoton karshe na kwamitin da aka kafa kan lamarin. Ya kara da cewa dole ne kasashe makwabta su kuma nuna jajircewa wajen dakile fasa-kwauri daga karshen su.

A halin yanzu, Osinbajo, da yake amsa tambaya kan ci gaba da rufe iyakokin kasa musamman a daidai lokacin da ake shirin kulla Yarjejeniyar Cinikin Kasashen Nahiyar Afirka, ya ce a ranar Alhamis cewa gwamnati na aiki tare da kasashen makwabta kan sharuddan sake budewa kan iyaka. Osinbajo, wanda ya yi magana a lokacin wani gidan TVn yanar gizo da The Africa Report ta shirya, mai taken, ‘Bouncing back:
ya ce, “Muna aiki tare da makwabta don ganin a kan wadanne sharudda za mu sake bude wadannan iyakokin. A yanzu haka, muna gudanar da sintiri na hadin gwiwa don sarrafa fasa-kwauri a kan iyakokin kuma muna ganin yana aiki kuma na tabbata cewa nan ba da jimawa ba ya kamata mu bude kan iyakokin. “Mun dukufa ga AfCFTA amma muna damuwa game da barazanar tsaro da tattalin arziki kuma dole ne mu dauki wasu matakai wadanda za su biya bukatun kasar mu kai tsaye Inji Osinbanjo

Tabbas (rufe iyaka) ba lallai bane ya kasance na dindindin ba kuma muna fatan sake budewa cikin sauri.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button