Tsaro
Labari mai daɗin ji, wasu riƙaƙƙun ‘yan bindiga sun ajiye makamansu sun miƙa wuya ga gwamnati a jihar Zamfara yau.
Yau da misalin karfe hudu dai dai Na yamma wasu fitattu kuma gagaruman’yan bindiga da suka addabi jihar zamfara sun yadda da makaman su a jihar zamfara.
Sun mika makaman nasu ne tare da tawagarsu a Gidan gwamnatin jihar ta zamfara.
Gwamnan zamfara matawalle ne ya karbe su tare da shan alwashin bada goyon baya wajen kawo karshen matsalar tsaro a jihar zamfara dama Arewa maso yamma gaba daya.
Daga Kabiru Ado Muhd