Labarai
Labari Mai Dadin ji: Kasar Ireland Ta Dawowa Da Najeriya Euro Miliyan 5.5 Na Abacha.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Kasar Ireland ta Dawowa da Najeriya Euro miliyan biyar da digo biyar, kwatankwacin Dalar Amurika Miliyan 6.5.
Wannan Makudan Kudin da aka dawowa kasar nan da su, Tsohon Shugaban Mulkin Sojan Kasar Janar Sani Abacha ne ya Kai su Ya boye a Kasar dama wasu kashen Turawa.
Ministan Shara’ar Kasar Ireland Helen McEntee ne Ya sanar da Maida Kudin Najeriya.
Kungiyar da ke kula da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya, Transparency International tace Abacha Ya saci Kudin Talakawa da yawansu yakai biliyan $5 a Tsawon Shekaru 5 Na Mulkinsa, Yakai Kasashen Waje Ya Boye.