Addini

Labarin gaskiyar Abinda ya faru a kasar Faransa.

Spread the love

  1. Wani malamin makaranta mai suna Samuel Paty ya nunawa yan ajinsa hotunan batanci da mujallar Charlie Hebdo ta yi ga Manzon Allah (saw).
  2. Daya daga cikin daliban mai shekara 18, Abdullah Anzorov, dan asalin Chechnya da yake a Faransa, ya tare malamin ya yankashi. Amma shi ma hukumar tsaro ta harbeshi nan take.
  3. Wannan ya janyo maganganu da suka shafi addinin musulinci da aiyukan ta’addanci a jaridu da shafukan sadarwar Faransa.
  4. Gwamnatin Faransa ta fadawa musulman kasar da suke da yawan miliyan biyar cewa za ta dinga kula da masallatai kuma za ta hana shigo da limaman da ake zargin suna koya ta’addanci.
  5. Gwamnatin kuma ta rufe masallaci guda daya da ake zargin yana da alaka da shi wannan matashi da ya yanka malaminsa. Sannan ta kama wasu limamai bakwai da ake zargin suna da alaka da shi ta hanyar yan ta’addan Syria saboda bincike.
  6. Duka abubuwan sama musulman kasar sun aminta da shi kuma masu saukin ra’ayi cikinsu sun yarda za su shiga harkokin gwamnati domin yin addini cikin salama, musamman tun da ta ce za ta tallafawa masu kokarin fahimtar da addini cikin saukin kai.
  7. Daga baya kuma sai Emmanuel Macron, shugaban kasar ta Faransa, ya yi wani bayani inda yake cewa musulinci yana cikin matsalar da ya alakantata da aiyukan yan ta’adda. Ya kuma nemi a kawo sauyi wajen koyar da addinin a duniya baki daya.
  8. Sannan ya ce kasar Faransa kasa ce da ta bayar da yancin ra’ayi don haka za a ci gaba da buga hotunan batanci da mujallar Charlie Hebdo ta saba yi.
  9. Wannan ya janyo masana a fadin duniya da kuma yan adawa a cikin gida suka caccaki shi Macron din da cewa ya bata rawarsa da tsalle. Domin cin zarafi daban haka kuma fadin ra’ayi daban. Zanen cin zarafi ne ba wai yancin ra’ayi ba.
  10. Kasashen duniya da yawa, ciki ko har da wasu kungiyoyi a Amurika, sun caccaki Macron da cewa fadinsa za a ci gaba da zanen zai kara ingiza wutar da dama akwaita kuma zai janyo har musulman da suka yi tur da kisan wancan malamin su janyo hannunsu karshe yan ta’adda su yi amfani da wannan damar wajen kai hare-hare.
  11. Ya zuwa yanzu dai shi Macron bai janye maganarsa ba. Kuma kasashen duniya na ci gaba da tur da rawarsa da ya bata da tsalle. Wasu daga ciki, musamman na Musulmi, sun yi kira da a dena siyan kayayyakin da ake yi a Faransa.
  12. Kasar Turkiyya ita ce kan gaba wajen kira da a dena mu’amala da Faransa. Kasar Saudiyya ana ganin har yanzu ba ta iya cewa a dena siyan kayan Faransa ba saboda alakarta da kasar ko kuma saboda rigimarta da Turkiyya.
  13. Labaran karya da jita-jita sun shigo lamarin da yawa. Don haka ya kamata a fadi abubuwan da suke faruwa ba wai a tashi hankali akan abin da ba a yi ba. Iya abin da aka yi ya isa a yi tur da shi ba sai an hada da karairayi ba.
  14. Maganganun cewar Macron yana zina da malamarsa kafin ya aureta tun yana yaro shirme ne. Bai kamata mu yaki karya da karya ba. Hotunan da ake yadawa na batanci ga Macron su ma ya kamata mu dakata saboda Allah ya hanamu zagin kafirai saboda sai su rama akan Allah! Daga Aliyu Dahiru Aliyu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button