Daga watan Janairun 2021 zuwa yanzu, an zuƙi tabar sigari sama da tiriliyan ɗaya a faɗin Duniya ~ Bincike

Binciken Worldometer ya tabbatar da tun daga farkon shigowar shekarar 2021 zuwa yanzu an zuƙi tabar sigari kimanin kara tiriliyan ɗaya. Hakazalika an zuƙi aƙalla kara biliyan shida cikin watanni biyu kacal. Kamar yadda cibiyar bincike ta Worldometers dake ƙasar China ta bayyana.

Ya zuwa loƙacin da ake tattara waɗannan bayanan; aƙalla tabar sigari 6,732,441,834 ake amfani da cikin kowacce rana ɗaya kacal.

Binciken ya ƙara bayyana yadda aƙalla mutane 1,717,911 suka mutu sakamakon shan tabar sigari daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu.

Har’ilayau, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) tabar sugari tana daga cikin cututtuka masu saurin haddasa rashin lafiya da kashe ɗan’ Adam cikin ƙanƙanen loƙaci, yayinda kuma a kullum ake samun kaso 7% na masu rasa rayukansu sakamakon cutar.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *