Dole ne kowane Gidan Mai ya tanadi na’urorin kashe gobara ko kuma ya fuskanci fushinmu – Ganduje.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi masu gidajen man fetur na Jihar Kano da su tabbatar sun tanadi
Na’urorin kashe gobara ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido don duba wadanda suka jikata sakamakon gobarar da akai a Gidan man Al-Ihsan dake unguwar sharada a Kano kwanan nan.

Idan baku manta ba a kwanakin baya mun kawo muku Rahoton yadda gobarar ta lakume mutane sama da 50, ciki har da ma’aikatan kashe gobara sama da 20.

Gobarar ta auku ne sakamakon kamawa da wuta da wata tankar man fetur tayi wadda ta kawowa gidan man fetur.

Babu shakka lamarin gobarar ya munana, yanzu haka wadanda suka jikkata suna kwance a Asibitin Murtala dake birnin Kano.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *