KIWON LAFIYA: An fara yiwa masu bautar ƙasa allurar rigakafin cutar COVID-19.

Ƙungiyar matasa masu bautar ƙasa wato NYSC ta sanar da fara yiwa mambobinta rigakafin allurar COVID-19 a yau Litinin.

A wata sanarwa ta musamman da Shugaban tsare-tsare na ƙungiyar mai suna Birgediya-Janar Shuaibu Ibrahim ya fitar, ya bayyana yadda aikin yake wakana a dukkan cibiyoyin ƙungiyar dake faɗin Nigeria.

Ƙungiyar ta NYSC ta bayar da umarnin karɓar allurar ga duk mambobin nata ne ta hanyar yin rijista a shafin ƙungiyar na yanar gizo-gizo.

Hakan ya biyo bayan umarni da hukumar lafiya ta bayar na tabbatar da anyi wa kowanne mamba allurar rigakafin cutar ba tare da ɓata lokaci ba; kamar kuma yadda aikin yake tafiya cikin nasara.

Mista Shuaibu Ibrahim ya ƙara da miƙa godiyarsu ga kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin kula lafiyar mambobin masu bautar ƙasa a sassa daban-daban na faɗin Nigeria.

A ƙarshe, NYCS ta bayyana a shafinta na yanar gizo-gizo bisa ga irin shirin da take na tabbatar da kowanne mamba, ma’aikaci da masu kula da harkokin ƙungiyar anyi masa rigakafin nan ba da jimawa ba.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *