Mun baiwa El-Rufai sa’o’i 48 domin ya gaggauta dawo da ma’aikatan lafiya da ya kora wuraren aikin su. ~ MHWUN

Ƙungiyar ma’aikatan lafiya (MHWUN) sun baiwa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai sa’o’i 48 domin ya gaggauta dawo da ma’aikatan lafiya mata waɗanda ya sallama kwanaki biyu da suka gabata.

MHWUN sun bayyana hakan ne ta wani bayani daya fito ta hannun Shugaban ƙungiyar Biobemeloye Joy Josiah, tare da bayyana matakin na Gwamnan a matsayin cin mutunci ga hukumar lafiya a fadin Jihar ta Kaduna dama ƙasa baki ɗaya.

Mista Josiah ya ƙara da cewa a baya-bayan nan na ma, Gwamnan ya tilastawa wasu ma’aikatan lafiya waɗanda shekarunsu suka wuce 50 domin su yi ritaya, wanda hakan baya daga cikin tsari na hukumar lafiya, amma a hakan El-Rufai sai da ya tilasta har suka ajiye ayyukan su.

A ƙarshe Shugaba hukumar lafiyar yayi kira ga ɗaukacin mambobin hukumar lafiya a faɗin Nigeria da su yi dakon matakan da zasu iya biyo baya idan har Gwamnan ya gaza jin kokensu “a cewar sa duk abinda ya shafi jami’in lafiya, ya shafi hukumar ne baki ɗaya.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *