Mutum 120 ne suka kamu da cutar COVID-19 jiya Talata a Nigeria.

An samu ƙarin mutane 120 waɗanda suka kamu da cutar COVID-19 a Nigeria jiya Talata, kamar yadda hukumar kula da sabbin cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana.

Duk da samun waɗanda suka ƙara kamuwa da cutar, a wani ɓangaren kuma an samu afuwa kamar dai yadda aka kwashe sama da kwanaki takwas a jere ba tare da samun wanda ya mutu sakamakon cutar koda mutum ɗaya a Nigeria ba.

Har’ilayau; an samu ƙarin mutum 120 ɗin ne a tsakanin jihohin Enugu-53, Lagos-22, Rivers-18, Ogun-80, FCT-7, Abia-6, Kano-5 da kuma jihar Bauchi mutum ɗaya.

Wannan ne ya kawo jumullar adadin mutanen da suka kamu wanda yawan su yakai 164,423; yayinda mutane aƙalla 2,061 suka mutu tun bayan ɓullar cutar a watan Fabrairun shekarar data gabata, 2020.

A kwanakin baya ma an fara rigakafin cutar ta COVID-19, wanda kawo yanzu an samu nasarar yiwa adadin mutane miliyan 3.94 a faɗin ƙasar; kamar yadda hukumar NCDC ta bayyana.

Rahoto; Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *