Wata matashiya ta kafa kungiyar tallafawa mata dan Samar da auduga

Easy Pad Movement ƙungiya ce da Hauwa Abdulraheem ta kafa, bayan yin rubutu game da rashin auduga na mata saboda damuwa. Hakan ya jawo hankalin mutane da yawa kuma ya taɓa zuciyar masu karatu adalilin hakan suka bata kwarin gwuiwa ta fara wannan kamfe. 

Ba da daɗewa ba, wacce ta kirkiro ta yanke shawarar zuwa gidaje don yin hira da ƙananan matan da take ganin ba za su iya ɗaukar nauyin siyan pad ba a yankinsu. A ranar farko ta hirar ne ta gane cewa ba wai kadan audugar kawai suke bukata bah, akwai bukatan wayar da ‘yan matan game da abunda ya shafi jinin haila. Wannan shine lokacin da tafiyar ta ɗauki sabon hanya. Rubutun da ke ƙasa sune abubuwan da aka gano;

1. An gano cewa kyamar jinin haila har yanzu tana da girma sosai.

2. Mafi yawan wadannan ‘yan matan suna da karancin sani ko kuma rashin ilimin tsafta.

3. Mafi yawa daga cikin wadannan ‘yan matan suna ganin jinin haila abin kunya ne.

4. Yawancinsu suna amfani da mugayen abubuwa yayin al’ada.

5. Yawancinsu basu taɓa yin amfani da pad ba. 

6. Kusan dukkansu ba za su iya tattaunawa akan jinin haila tare da iyayensu mata ba.

Kungiyar Easy Pad ta ɗauki sabon hanya kuma manufarta ta faɗaɗa. Menene makasudin kungiyar Easy Pad movement?

1. Manufar farko ta Easy Pad Movement ita ce a bai wa wasu yara ‘yan mata pads na watanni maimakon sau daya.

2. Don wayar da kan mata game da jinin al’ada da tsaftar jinin al’ada.

3. Koya wa wadannan ‘yan mata yadda ake amfani da pad din da aka basu.

4. Badawa mata akalla su hamsin a ko wata jiha pad na tsawon wata biyar

Tafiyar tana samun tallafi daga gudummawar jama’a kuma rabon farko da aka fara, anyi shi ne a ranar Asabar, 24 ga Afrilu inda aka ba ‘yan mata 32 kunshin pads biyu kowannensu. Wannan rarrabawar ya faru ne a Zariya.

Ma’aikatan lafiya biyu sun yi farin ciki da shirin ciki har da Wanda ya assasa sarauniya Girl Child foundation. Sun tattauna gabaɗaya game da al’ada da tsafta. Hakanan, an koyar dasu kan yadda ake sa pad. Any budadden Tattaunawa inda ‘yan matan suka yi tambayoyi. Bayan tattaunawar, an rarraba audugar ga ‘yan mata 32.

A ƙarshen shirin, ‘yan matan cikin nutsuwa yi tambayoyi. Wasu daga cikinsu sun kasance masu jin kunya saboda watakila shine karo na farko da suke tattaunawa game da jinin al’ada acikin jama’a.

Ga yawancin waɗannan ‘yan matan, yin amfani da audugar kamar mafarki ne.

Da yawa daga cikinsu suna zama a gida yayin al’adarsu saboda sun gwammace suyi rashin karatu fiye da zuwa makaranta suyi datti. Ma’aikatan lafiya sun yi bayani mai tsawo kan yadda wadannan ‘yan mata za su iya tafiyar da rayuwar su a yakin da suke aladar su. Sun tattauna illar rashin kula da kai lokacin da ake yin al’ada.

Easy Pad Movement yana neman gudummawar jama’a don cimma burinta. Ba za mu iya taimaka wa duk yarinya ba, amma za mu iya taimaka wa da yawa.

Daga Maryam Ango

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *